10 Satumba 2025 - 16:58
Source: ABNA24
An Gudanar Da Mauludin Manzon Allah {A} A Abuja + Hotuna

Harkar Musulunci karkashin jagorancin Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) ta gudanar da gagarumin muzaharar 17 ga watan Rabi'ul Auwal, wanda shine muzaharar Maulidi da aka saba gudanarwa a duk shekara.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: An fara muzaharar Maulidin a cikin wani anguwa mai suna Fish Market dake Apo" sannan aka fito da muzaharar zuwa wani babban junction inda anan aka rufe, bayan kammala muzaharar yan'uwa sun fara watsewa sai ga jami'an tsaro mota biyu Mopol da police suka fara wuce 'yan uwa sai suka samu wani waje suka tsaya suka fara harbi da harsasai masu rai.

Zuwa hada wannan rahoton bamu da tabbacin wanda aka harba, ko aka kama" abun da muka sani anyi muzaharar Maulidin Manzon Allah (S.A.W.W) a Abuja, koda Azzalumai basu so ba.

Mai Rahoto: Isa Charis 

AliAssajjad Ibn Taheer 

10th/Sept/2025

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha